Yayin da Amnurka ke fatan ganin an cimma matsaya a zaman tattaunawar da ake yi da kungiyar Taliban nan da zuwa watan Staumba, masu fashin baki da jami’an kasar Afghanistan sun fara nuna shakku kan ko za a iya samun kwakkwarar matsaya.
Masu fashin bakin na tarabbabi ne kann cewa, gwamnatin ta Afghanistan ba ta samu damar yin wata tattaunawa ta kai-tsaye da kungiyar ta Taliban ba.
A watan da ya gabata ne, sakataren harkokin wajen Amurka, Mike a Pompeo yayin wata ziyara da ya kai a Afghanistan da kuma sauran yankin, ya ce, Amurka na fatan ganin an kulla wata yarjejeniyar zaman lafiya nan da 1 ga watan Satumba mai zuwa.
Sai dai wasu masu sa ido kan rikicin na Afghanistan, na hasashen cewa zai yi matukar wuya a iya cimma matsaya, amma suna ganin za a iya samun daidaito kan batun janye dakarun Amurka daga kasar ta Afghanistan.