Wadanda suka tsira daga aman wutar Fuego a kasar Guatemala sun fara zaman makokin mutanen da aka gano gawarwakinsu yau Talata bayan da aman wuta, da iskar gas da kuma barbashin duwatsu suka kashe akalla mutane 69, toka da laka kuma suka lullube kauyukan dake kusa da wurin.
Wani gidan talabijin na kasar ya nuna masu makokin suna dauke da makarar mamatan akan kafadunsu. Yayinda ma’aikatan agaji ke cigaba da neman wadanda ke raye, hukumomin kasar sun kara adadin wadanda suka mutu yayinda ake gano gawarwakin mutane daga baruguzan duwatsu a kewayen kauyukan da bala’in ya fi shafa. Hukumomin kuma sun ce ta yiwu adadin wadanda suka mutu ya kara hawa.
Jami’an dake kiyaye bala’i sun ce aman wutar da ya faru ranar Lahadi ya shafi fiye da mutane miliyan daya, an kuma kwashe wasu su 3,265 daga wuraren da aman wutar ya faru, sannan an kai mutane 20 da suka jikkata wasu cibiyoyin kiwon lafiya
Facebook Forum