Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Watsi Da Ayyuka Sama Da Dubu 13 A Yankin Neja Delta - Akpabio


Nigerian Minister of Niger Delta, Godswill Akpabio
Nigerian Minister of Niger Delta, Godswill Akpabio

Ministan hukumar kula da yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa a halin yanzu akwai ayuka sama da dubu 13 da aka yi watsi da su a yankinsa.

Sanata Akpabio ya bayyana hakan ne a lokacin da ya mika rahoton kwamitin binciken kwakwaf da ya gudanar da bincike a kan zargin yin zagon kasa da ake yiwa hukumar raya yankin Neja Delta wato NDDC ga shugaba Muhammadu Buhari, ta hannun ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami.

Rahoton kwamitin binciken ya nuna cewa akwai ayuka sama da dubu 13 da aka yi watsi da su a yankin Neja Delta kuma tun kafin gabatar da rahoton, wasu ‘yan kwangila sun koma kan aikin su da kan su kuma sun kammala ayyukan hanyoyi kimanin 77.

Akpabio ya kara da cewa ba'a yi aikin binciken don yiwa wani bita da kulli ba, amma don tabbatar da cewa an yi amfani da dimbin kudaden da aka ware don gudanar da ayyukan bunkasa yankin ta hanyoyin da suka dace.

A cewarsa, yankin Neja-Delta ya ci gaba da zama cikin koma baya tun shekarar 1958 duk da kokarin da gwamnatocin baya suka yi ta hanyar kirkirar shirye-shirye da ayyuka daban-daban, yanayin da ya ce yana canzawa.

A halin da ake ciki dai shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatin Najeriya za ta tabbatar ta kwato sama da naira tiriliyan 6 da ake zargin an karkatar da su wajen gudanar da ayyukan hukumar NDDC tsakanin shekarar 2001 zuwa 2019.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne bayan ya karbi rahoton binciken kwakwaf daga hannun sanata Akpabio a ranar Alhamis inda ya yi ikirarin cewa akwai tabbatattun hujojji da suka yi nuni da cewa akwai akalla ayuka dubu 13,777 da ba’a aiwatar yadda ya kamaşa ba da kuma gano dimbin asusun bankin na hukumar NDDC da suka kai 362 wanda ba’a ba da daidaiton bayani a kan su.

Haka kuma, shugaba Buhari ya ba da umarnin a mika rahoton binciken da aka yi kan hukumar NDDC ga ma’aikatar shari’a ta tarayya don daukar matakin da ya dace.

Bayan karbar rahoton ministan shari’a Abubakar Malami, ya ba da tabbacin cewa za'a yi nazari sosai don aiwatar da ayukan da suka dace.

Idan ana iya tunawa, a watan Oktobar shekarar 2019 ne shugaba Buhari ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan ayyukan hukumar NDDC tun daga lokacin da aka kafa ta har zuwa watan Agustar shekarar 2019.

Wannan kuma martani ne ga bukatun al’umman yankin don ganin hukumar ta yi aiki mai inganci da kuma samun sakamako mai kyawu.

XS
SM
MD
LG