WASHINGTON, D. C. - Lamarin dai ya zama abin bacin rai ga shugaba Recep Tayyip Erdogan, wanda da ya sa aniyarsa ta sake samun iko a wadannan garuruwa.
An kirga sama da kashi 90% na akwatunan zabe, magajin birnin Istanbul mai ci Ekrem Imamoglu, na jam'iyyar Republican People's Party, ko CHP, yana kan gaba da tazara mai yawa a birni mafi girma da tattalin arziki a Turkiyya, a cewar kamfanin labarai na kasar Turkiyya na Anadolu.
Mansur Yavas magajin garin Ankara babban birnin kasar, ya ci gaba da rike kujerarsa tare da tazarar maki 25 akan abokin hamayyarsa, kamar yadda sakamakon ya nuna.
A cewar Anadolu, jam'iyyar CHP ta lashe kananan hukumomi 36 daga cikin larduna 81 na Turkiyya, inda ta yi kutsawa cikin yankuna da dama na jam'iyyar Erdogan.
Ta samu kashi 37% na kuri'un da aka kada a fadin kasar, idan aka kwatanta da kashi 36% na jam'iyyar shugaban kasa, wanda ke nuna nasarar zaben jam'iyyar CHP mafi girma tun bayan hawan Erdogan kan karagar mulki shekaru ashirin da suka gabata.
Erdogan ya amince da koma bayan zaben a wani jawabi da ya gabatar daga barandar fadar shugaban kasar, yana mai cewa jam'iyyarsa ta yi asarar babban matsayi a fadin kasar Turkiyya.
Mutanen sun isar da “sako” wanda jam’iyyarsa za ta “nazarta” ta hanyar “karfafawa” sukar kai, in ji shi.
Erdogan ya kara da cewa, "Abin takaici, watanni tara bayan nasarar da muka samu a zaben na ranar 28 ga watan Mayu, ba mu iya samun sakamakon da muke so a gwajin zaben kananan hukumomi ba." "Za mu gyara kurakuranmu kuma mu gyara kuskuren mu."
Ya sha alwashin ci gaba da shirin tattalin arziki da aka bullo da shi a bara wanda ke da nufin yaki da hauhawar farashin kayayyaki.
Dandalin Mu Tattauna