Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Mu Da Niyyar Cafke Shugaban Hukumar Zaben Najeriya - DSS


Shugaban hukumar zabe - INEC Farfesa Yakubu Mahmood
Shugaban hukumar zabe - INEC Farfesa Yakubu Mahmood

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya wato DSS, ta ce bata wani yunkuri don cafke shugaban hukumar zaben kasar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu

ABUJA, NIGERIA - DSS cikin sanarwar da ta aikewa sashin Hausa na Muryar Amurka da kakakinta Dr Peter Afunyaya ya sanyawa hannu, ta ce wata jaridar kasar ta jirkita ainihin abin da ya faru a kotu, inda ta wallafa labarin ba kamar yadda yake ba.

Sanarwar ta ce, ya zama wajibi ta yi wannan jan hankali, domin labarin da jaridar ta wallafa kwata-kwata ba haka bane, ba gaskiya bane cewa hukumar DSS taje kotu don neman ikon kama shugaban hukumar zaben.

Hedikwatar Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta Najeriya DSS
Hedikwatar Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta Najeriya DSS

DSS ta ce tana sane da yunkurin wasu marasa kishin kasa na ganin sun haddasa rikici a cikin kasa ta hanyar haddasa rudani dangane da babban zabe da za ayi a Najeriya cikin wannan shekara.

Sanarwar ta kara da cewa, daya daga cikin wannan hanyar kawo rudanin ita ce haddasa wani irin mummunan yanayin siyasar da kuma son yin amfani da sashin shari'a wajen ganin an kawo wa jami'an tsaro cikas wajen gudanar da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Jami'an Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya a Gaban Majalisar Dokokin Najeriya a Abuja
Jami'an Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya a Gaban Majalisar Dokokin Najeriya a Abuja

Hukumar tsaro ta DSS din ta aika da sakon gargadi mai zafi ga duk wadanda ke son ganin sun kawo rudu ga babban zaben da za ayi,

Kazalika ta kuma shawarci al'umma da a yi taka tsantsan, domin gudewa kawo cikas ga zaben, yayin kuma da take tabbatar da za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta tabbatar da samar da kyakkyawan yanayin tsaro don samun yin zabe na gaskiya mai cike da adalci, DSS ta kuma nemi hadin kan baki da ‘yan Najeriya don cimma manufar.

XS
SM
MD
LG