Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar Jam'iyyar MNRD Ta Musanta Batun Canza Sheka


 Seni Oumarou shugaban jam'iyyar MNRD da Mahammadou Issoufou shugaban Nijar na jam'iyyar PNSD
Seni Oumarou shugaban jam'iyyar MNRD da Mahammadou Issoufou shugaban Nijar na jam'iyyar PNSD

Makon jiya ne jam'iyyar MNSD ta balle daga kwancen adawa ta karbi goron gayyatar shiga gwamnatin hadin gwuiwa da shugaban kasar Mahammadou Issoufou ya kuduri kafawa, saboda wai, a warware matsalolin da suka addabi kasar

Jita jitar da ake yayatawa na cewa jam'iyyar ta MNRD tana shirin yiwa jam'iyyar MNSD zago kasa saboda shigarta gwamnatin PNSD ya sa ta fitar da wata sanarwa.

Sun musanta batun cewa suna shirin canza sheka zuwa PNDS saboda dangantaka dake tsakanin shugaban kasa da shugaban jam'iyyar ta MNRD, abun da ta kira shati fadi.

Alhaji Sedu Yakuba mataimakin shugaban jam'iyyar MNRD Hakuri yace 'yan Nijar na ciki da na ketare su sani babu wani shirin canza sheka. Yace MNRD Hakuri tana nan gungunta na adawa.

Yace idan ana tafiyar siyasa a kasa ya kamata a ce akwai adawa. Idan an yi la'akari a lokacin da suka gabatar da Mahamman Usman a matsayin dan takara kokari aka yi a takure ko a tauye dimokradiya a kasar

Mahamman Usman dan karar jamiyyar MNRD
Mahamman Usman dan karar jamiyyar MNRD

Inji Mahamman Usman tsayar da dankarar da suka yi ya ba dimokradiya dagalaba. Haka ma a wannan tafiya da ake yi sun lura cewa wannan gwamnati ta Mahammadou Issoufou so tak yi ta mayar da adawa gefe guda. Yace su jam'iyyarsu ta matasa bata yadda da kawar da adawa ba.

To saidai jam'iyyar PNDS Tarayya ta musanta yunkurin durkusar da dimokradiya a karkashin shirin gwamnatin hadaka kamar yadda kakakinta Asumana Muhammadou ya fada. Yace duk wadanda suka san ciwon kasa sun amshi gayyatar shugaban kasa kamam irinsu MNSD.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG