Shugaban hukumar tarrayar turai Jean-Claude Juncker yana kira ga galibin kasashen turai su amince da adadin ‘yan gudun hijirar da zasu rika karba cikin shekaru biyu masu zuwa, daga dubban masu neman mafaka dake kwarara daga gabas ta tsakiya.
Shirin zai iya bada dama ga kimanin ‘yan gudun hijira dubu dari da sittin, da mafiya yawa zasu tafi Jamus, da kuma Spain, biye da su kuma sai kuma Poland da Netherlands da Romaniya da Belgium da kuma Sweden.
Yayinda kasashen turai ke fuskantar kwararar ‘yan gudun hijira mafi girma tun yakin duniya na biyu, Juncker zai bayyana cikakken shirin da yake dashi gaban majalisar tarayyar turai yau laraba. Sai dai kasar Hungary da wadansu kasashen turai basu goyi bayan tilastawa kasashe yawan ‘yan gudun hijiran da zasu karba ba. Babu tabbacin tasirin tsarin kimantawa kasashe adadin ‘yan gudun hijirar da zasu karba, yayinda tuni shugabannin kasashen turai suka shure bukatar aza masu nauyin karbar ‘yan gudun hijira dubu arba’in kawai.
Za a aiwatar da sabon tsarin raba masu neman mafakar ne bisa ga karfin tattalin arzikin kasa, da yawan al’umma da guraban ayyuka da kuma yawan ‘yan gudun hijiran da kasashen suka riga suka tsugunar.
Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel, kasar da ta tarbi ‘yan gudun hijiran da abinci da ruwan sha da kuma kayan wasan yara, ta bayyana shirin Juncker a matsayin muhimmin matakin farko. Tace bin tsarin KTT na tantance masu neman mafakar a tashar jiragen ruwa lokacin da suka iso ba zai yiwu ba yanzu, sabili da yana nufin kasar Girka ce zata dauki nauyin ‘yan gudun hijiran dake kauracewa kasashen gabas ta tskiya da kuma Afrika.