A tattaunawarsa da wasu jaridun kasar ne a jiya ne, Jami’in, mai suna Col. Htein Linn, wanda shine ministan tsaro da harkokin iyaka na jihar Rikhine, yake cewa zasu rusa masallatan da wasu gine-gine ne da ba a ginasu da izinin dokokin kasar ba.
Wani mukarrabinsa ya shaidawa Muryar amurka cewa wannan ministan da Shugaba kasar, Aung Sang Suu Kyi ce ta nada, shine aka baiwa aikin sake dubawa da rusar da gine-gine da hukuma bata san dasu ba.
Ana kiyasin cewa akwai gine-gine kamar 2,270 da aka gina ba a biosa ka’ida ba a kasar, wadanda suka hada harda masallatai 9 da makarantun islamiyya 24 a daya daga cikin garuruwan da abin ya shafa mai suna Maungdawo, yayinda ake da wasu gine-gine sma da dubu daya da suka hada da masallatain 3 da makarantun islamiyya 11 da aka kafa su ba bisa ka’ida ba a gari na biyu mai suna Buthidaung.
Jihar Rakhine tana cikin jihohin kasar Burma masu fama da talauci inda musulmi dubu dari da ashirin da biyar ke zaune wanda akasarinsu suke zama a cikin gine-ginen wucin gadi biyon bayan tashe-tashe hankulan da aka yi tsakanin mabiya addinin Buddha da Musulmi inda kuma aka yi asaran rayukka da yawa a shekarar 2012.