A cikin wata wasikar da kamfanin dillancin labaran Reuters ya bankado, shugaban ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya a D.R. Congo Leila Zerrougui, tace tana rubuta wannan wasikar domin sanar da babban sakataren Majalisar wani labari mai damuwa, inda aka samu wani abokin aikita a wani sansani a Beni ya kamu da cutar Ebola, wanda a halin yanzu ana kula da jinyarsa.
Zerrougui tace wannan ma’aikaci ya kwashe makwanni bai zuwa aiki, daga nan ne aka fara neman inda yake.
Wannan labarin ya biyo bayan kashedi ne da jami’an kiwon lafiya suka yi a kan yanda sabuwar ebolar take yaduwa cikin gaggawa kuma adadin wadanda suka kamu zai iya ninka abinda aka gani a cikin Satumba.
Ma’aikatar kiwon lafiyar D.R. Congo tace ya zuwa jiya Juma’a wadanda suka mutu sun kai 125, a cikin mutane 201 da suka kamu da kwayar cutar, kana an kuma tabbatar da mutane 166 sun harbu da ma wani karin wasu 35.
Facebook Forum