A Jamhuriyar Nijar kungiyar kasa da kasa ta Plan International Niger ta kaddamar da wata yekuwar musamman da nufin fadakar da jama’a game da muhimmancin baiwa ‘yan mata damar morar ‘yancin da dokokin cikin gida dana kasa da kasa suka yi tanadi domin su.
A yayin bukin tunawa da ranar ‘yan mata ta duniya da ake gudanarwa a kowace ranar 11 ga watan Oktoba, kungiyar Plan Niger ta kaddamar da wannan kamfe dake fatan isar da sakwanni zuwa ga al’uma a karkashin wani sabon shirin da aka yiwa lakabi da Aux Filles L’egalite, dake nufin baiwa ‘yan mata dama kwatan kwacin wace aka saba baiwa samari kamar yadda wakilin wannan kungiya a Nijar Henri Noel ya bayyana.
Zasu fara Kamfen wanda zai gudana a dukkan sassan kasa, wanda wani lokaci ne na jan hankulan mahukunta da shuwagabanin al’uma wato sarakuna da malaman addinai da jami’an fafutika akan bukatar tasu gudunmowa don kawo karshen wahalhalun ‘yan mata a fannonin rayuwa inji Moustapha Ibrahim jami’in tsare tsare a Plan Niger.
Shugabar kungiyar ‘yan jarida masu kare hakkin jama’a a fannin kiwon lafiya Hajiya Amina Hashimu wace ta halarci bukin kaddamar da wannan yekuwa ta yaba da wannan tsari sai dai tana mai nuna damuwa akan wasu abubuwan da ka iya biyo baya.
Kungiyoyin kare hakkin yara sun bayyana jamhuriyar Nijar a matsayin kasar da tafi kowace kasa aurar da yara kanana a duniya, lamarin da ake dauka a matsayin wadanda ke sahun gaban dalilan da ke haddasa cikas wa lafiyar ‘yan mata, yayin da hakan ke hana masu samun ilimin zamani, abinda a karshe ke zama musabbabin talaucin dake addabar rukunin mata anan Nijar inji kungiyar Plan Niger.
Facebook Forum