Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jacksonville nan Amurka mutane uku sun mutu cikin wadanda aka harba


'Yan sanda a jihar Florida sun yiwa inda aka kai harin kawanya
'Yan sanda a jihar Florida sun yiwa inda aka kai harin kawanya

Dan bindigan da ya kai hari, David Katz tare da mutane biyu ne suka mutu yayinda sauran wadanda suka jikata na jinya a asibiti a garin Jacksonville dake cikin jihar Florida

Hukumomin jihar Florida sun ce mutane uku ciki harda dan bindigan da ya kai hari sun mutu, bayan harbin fada kan mai uwa da wabi, da aka yi a wasu kantunan da suke garin Jacksonville a jihar ta Florida

Tunda farko kafofin yada labaru sun bada rahoton cewa mutane hudu ne suka mutu, to amma shugaban yan sandan Jacksonville Sheriff Mike Williams ya ce rahotanin ba gskiya ne ba.

Sheriff Williams ya ce mutane tara ne suka ji rauni, a sakamakon harbinsu da aka yi, ciki harda mutane biyu wadanda suke suka tuka mota da kan su suka je asibiti. Yace an yiwa dukkan mutane taran jinya kuma suna murmurewa. Haka kuma mutane biyu sun ji rauni a lokacinda suke kokarin arcewa harbin da ake yi.

Sheriff Williams ya ce ana kyautata zaton maharin,shekarun sa ashirin da hudu ne, kuma sunansa David Katz daga garin Baltimore a jihar Maryland kuma ya kashe kan sa. Sheriff Williams bai bada wani karin haske dangane da dalilin yin harbe harben ba, amma yace kila nan da yan sa’o’i za’a samu karin bayani akan David Katz.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG