Washington, DC —
A wannan makon mun kawo kashi na hudu na hirar wakilinmu Mansur Nasir da wani fitaccen mawaki a Jamhuriyar Nijar Abubakar Abdu -Bappa Yaro wanda a shirin na yau, ya bayyana irin ci gaban da aka samu a fuskar waka.
Mun kuma bada labarin wani magidanci da ya yanke hukumci zai gudanar da daya daga cikin wadansu ayyuka biyu ko ta halin kaka.
Saurari cikakken shirin domin jin yadda ta kaya:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.