Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NCDC Ta Yi Gargadi Game Da Barkewar Bullar Cutar Ebola


Jami’an kula da lafiyar matafiya na duba fasfo kafin su yi amfani da ma’aunin zafin jiki su yiwa Mahajjata gwajin cutar Ebola.
Jami’an kula da lafiyar matafiya na duba fasfo kafin su yi amfani da ma’aunin zafin jiki su yiwa Mahajjata gwajin cutar Ebola.

Hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC ta sabunta gargadi ga ‘yan Najeriya game da yiwuwar barkewar cutar Ebola ta Sudan (EVD) a Uganda tun lokacin da aka fara ayyana ta a hukumance a ranar 20 ga Satumba 2022.

Ya zuwa ranar 29 ga Oktoba 2022, Ma'aikatar Uganda Hukumar lafiya ta kasar ta bayar da rahoton mutane 128 da aka tabbatar sun kamu da cutar sannan 34 sun mutu.

Dangane da bayanan da ake da su da kuma kimanta hadarin da aka gudanar, Najeriya na cikin babban hadarin shigowa da kwayar cutar.

Wani jami’in kula da lafiyar matafiya na amfani da ma’aunin zafin jiki ya na yiwa Maniyyata gwajin cutar Ebola.
Wani jami’in kula da lafiyar matafiya na amfani da ma’aunin zafin jiki ya na yiwa Maniyyata gwajin cutar Ebola.

NCDC ta ce ganin yadda ake yamutsa fasinjojin kasashen Najeriya da Uganda a filayen jirgin sama tsakanin Najeriya da Uganda, da kuma cakuduwar fasinjoji, musamman a wuraren tafiye-tafiye na yankin Nairobi, Addis Ababa, da filayen tashi da saukar jiragen sama na Kigali, akwai matukar hadarin yiwuwar cutar ta shigo Abuja cikin sauki.

Hukumar ta ce tuni ta dauki matakan kariya don ganin ba a samu yaduwar cutar ba, yayinda sashen na tunkarar annoba ke cikin shirin ko ta kwana don fara ayyukan shirye-shirye a cikin ƙasa.

Matakan rigakafin don rage tasirin yiwuwar bullar cutar ta EVD a Najeriya sun hadda da bin sawun fasinjojin da suka taho daga Uganda da wadanda suka yi tafiya zuwa kasar Uganda tsawon kwanaki 21 bayan sun isa Najeriya.

XS
SM
MD
LG