Karamar kasar ta tsakiyar Afirka mai kusan mutane miliyan 1.6 ta ba da rahoton mutuwar mutane tara da wasu 16 da ake tsammanin sun kamu da cutar bayan da aka dawo da wani samfurin da aka aika zuwa dakin gwaje-gwaje a Senegal a ranar 7 ga Fabrairu da ya tabbatar da akwai kwayar cutar.
Ministan kiwon lafiya Mitoha Ondo'o Ayekaba ya shaidawa manema labarai cewa, an fitar da sanarwar fadakarwar kiwon lafiya a lardin Kie-Ntem da kuma gundumar Mongomo da ke makwabtaka da lardin, bayan tuntubar Hukumar Lafiya ta Duniya da Majalisar Dinkin Duniya, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa.
Mutune taran sun mutu ne tsakanin 7 ga Janairu zuwa 7 ga Fabrairu, in ji Ayekaba.
Kwayar cutar Marburg ta kashe kimanin kashi 88 cikin dari na wadanda suka kamu da ita kuma tana yaduwa daga mutum zuwa mutum ta hanyar hada jiki da ruwan jik kai tsaye, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya. Cutar ta fito ne daga nau’in kwayoyin cutar Ebola. Alamun sun hada da zazzabi mai karfi da ciwon kai mai tsanani, inda majiyyata da yawa ke samun alamun ciwon fitar jini a cikin kwanaki bakwai.
WHO ta ce an tura jami'ai a Equatorial Guinea don bibiyan yaduwar cutar, da kebe masu cutar da kuma ba da kulawar lafiya ga mutanen da ke nuna alamun cutar."
Dokta Matshidiso ya ce "Marburg na da saurin yaduwa. Godiya ga ma’aikatan ko-ta-kwana da matakin gaggawa da hukumomin Equatorial Guinea suka dauka na tabbatar da bullar cutar, sannan ba da agajin gaggawa zai dakile cutar cikin sauri domin mu ceci rayuka da kuma dakatar da kyaduwar cutar da wuri-wuri," in ji Dr. Matshidiso Moeti, darektan Hukumar Lafiya ta Duniya na yankin Afirka.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce a halin yanzu babu alluran rigakafi ko maganin jinyar cutar.