Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa Na Zaben Sabon Shugaba Tsakanin Trump Da Harris


Jama'a a fadin Amurka su na kada kuri'a a ranar karshe ta zaben shugaban kasar na 2024. Tuni miliyoyin 'yan kasar suka kada kuri'unsu da wuri kafin ranar zaben, Talata.

Masu zabe a Amurka zasu yanke hukunci a yau bayan wani zabe mai cike da sammatsi da ka iya mayar da Kamala Harris ta zamo shugabar Amurka mace ta farko a tarihi ko kuma ya baiwa Donald Trump damar yin kome abin da ke razana duniya.

A yayin da aka bude rumfunan zabe a fadin Amurka a ranar zabe, ‘yar takarar jam’iyyar Democrat mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris, mai shekaru 60 da dan takarar jam’iyyar Republican tsohon shugaban kasa Donald Trump, mai shekaru 78, sun yi kankankan a takarar shugaban Amurka mafi rashin tabbas a zamanin da muke ciki.

Abokan hamayyar sun shafe ranaikun karshe na yankin neman zabensu suna kokarin yiwa magoya bayansu kaimi domin su fito suyi zabe tare da kokarin shawo kan duk mai niyar zaben da bai yanke dan takarar da zai zaba ba a jihohin rabagardamar da ake sa ran zasu sauya alkaluman zaben.

An bude rumfunan zabe da msalin karfe 6 na safe a jihohin dake gabar gabashin Amurka kuma ana sa ran milyoyin masu zabe su kada kuri’unsu, kari akan fiye da mutum milyan 82 da suka riga suka yi zabe a makonnin da suka gabata.

Za’a shafe kwanaki kafin sanin sakamakon karshe idan har aka yi kankankan kamar yadda zaben ke nunawa, inda yake kara zaman dardar a kasar dake fama da rabuwar kannu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG