Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa yanzu ta sahalewa dillalan mai su kulla cinikin fetur kai tsaye da matatar Dangote ba tare da bi ta hannun kamfanin man kasar NNPCL ba.
Hakan na zuwa ne kasa da kwana guda bayan da kungiyar dillalan man fetur din Najeriya masu zaman kansu (IPMAN) ta kalubalanci NNPCL game da sayar wa mambobinta da litar fetur a sama da Naira 1000, inda ta koka da cewar shi kamfanin na siyo litar man daga matatar Dangote a kasa da Naira 900.
Sai dai, a sanarwar daya fitar a yau Juma’a, Ministan Kudin Najeriya kuma shugaban kwamitin aiwatar da shirin sayar da danyen mai da Naira, Wale Edun, yace yanzu dillalan na iya sayen fetur kai tsaye daga matatun kasar na cikin gida.
“Daga yanzu, dillalan fetur na iya sayen man kai tsaye daga matatunmu na gida ba tare da NNPCL ya shiga tsakani ba. Muna karfafa gwiwar dillalan dasu kulla ciniki kai tsaye tsakaninsu da matatun akan farashin da suka aminta dashi, wanda hakan zai bunkasa gogayya tare da inganta kasuwanci.”
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake karin haske game da kaddamar da shirin sayar da danyen mai a Naira.
Rahotannin sun ce kwamitin aiwatar da shirin sayar da danyen mai da albarkatun da aka tace daga gare shi da Naira ya gudanar da ganawar nazarin yadda shirin ke tafiya a karo na 2 a ranar 10 ga watan Oktoban da muke ciki domin auna irin ci gaban da aka samu.
Dandalin Mu Tattauna