A jiya Laraba, kungiyar kwadago ta NLC ta yi fatali da sabon karin farashin man fetur din da aka yi, inda tace hakan zai kara ta’azzara halin talaucin da ake fama da shi a Najeriya.
“Karin farashin man zai kara sabbaba talauci kasancewar abinda masana’antun ke samarwa ya ragu, ga kuma mummunan tasirin da hakan zai haifar sakamakon rasa karin guraben aikin yi”, a cewar shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, a sanarwar daya fitar.
Ya kara da cewa “a bisa wadannan dalilai, muna kira ga gwamnati da ta gaggauta janye karin kasancewar wadanda aka yi a baya ma basu haifar da da mai ido ba. Babu abinda hakan zai haifar illa kara talauta al’umma”.
Nan take galibin gidajen man da ba mallakin kamfanin nnpcl ba suka bi ta hanyar kara farashin man, inda yawancinsu suka rika sayar da lita a kan Naira 1, 050 a sassa da dama na jihar Legas.
Gidajen man kamfanin NNPCL sun mayar da nasu farashin zuwa Naira 998 a jihar Legas da kuma Naira 1,030, a Abuja a jiya Laraba.
Dandalin Mu Tattauna