Taba sigari ta na zamewa wasu mutane jaraba. Bincike ya nuna shan taba sigari ya na iya kawo cutar sankara, da ciwon zuciya da sauran munanan cututtuka. Haka zalika, shan taba ya na iya hana mata daukan ciki sannan ya ragewa maza karfin sinadaren haihuwa.