Rasha da Belarus sun kaddamar da atisayen hadin gwiwa a wani sabon mataki da ake gani hukumomin Moscow ke yi, na nuna karfin soji a kusa da iyakar Ukraine, yayin da Amurka ke kara ba kawayenta na nahiyar turai tabbacin cewa, akwai tsauraran takunkumai da za a kakabawa Rasha, muddin ta mamaye Ukraine, inda har shugaba Biden ya gana da shugaban gwamnatin Jamus kan wannan batu.