Hukumar samar da ayyukan yi ga jama'a ta Najeriya, NDE, ta ce zata horas da matasa 'yan gudun hijira su dubu 11 da 600 a kan sana'o'i dabam-dabam da suka zaba da kawunansu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Darekta-janar na hukumar ta NDE, Dr. Nasiru Ladan Mohammed, shi ne ya bayyana wannan a Maiduguri a lokacin da yake ganawa da 'yan jarida.
A lokacin da yake amsa wata tambayar wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu, darekta janar din yace akwai wani shirin da suka yi wanda a lokaci guda suka koyar da matasa har dubu 76 da 400 daga jihohi dabam-dabam na Najeriya a kan sana'o'i na hannu domin su samu sukunin dogara da kai.
Yace wasu jihohi sun samu gurabu dubu 2, wasu kuma 4 a karkashin shirin.
Dangane da wannan shiri na musamman na horas da 'yan gudun hijira da yace matasa maza da matra su dubu 11 da 600 zasu ci moriya, Dr. Nasiru yace wasunsu, musamman mata a Borno, sun nemi da a koya musu dinkin huluna, wasu kayan shafe-shafe da turare da toka ta wanka da ta wankin kaya da kayan yaji da sarkoki.
Yace jami'an hukumar dake jihohi da yankuna, sune suka jagoranci rarraba takardun neman shiga wannan shirin da aka raba, matasan kuma suka cike suka maido.
Darekta janar din yace tun wata gudan da ya shige, suka riga suka turo kudaden alawus da za a biya matasan da zasu koyi sana'ar da kuma wadanda zasu koya musu wadannan sana'o'i.
Ga cikakken rahoton Haruna Dauda Biu...
Facebook Forum