‘Yan kasar da dama na ganin cewa zaman lafiya da kwanciyar hankalin da jamhuriyar Nijer ta samu wata gagarumar nasara ce da ya kamata ‘yan kasar su yaba da shi.
Jama’ar da dama sun bayyana wasu daga cikin ayyukan gyaran kasa da shugaban ke yi, kamar layin dogo da kokarin inganta tsaro da yaki da ta’addanci da kuma sauran ayyuka makamantansu.
A daya bangaren kuwa jama’ar sun koka ne akan rashin samar da abubuwan more rayuwa da gwamnatin ta alkawarta masu a lokacin da take yakin neman zabe, da kuma abinda suka bayyana a matsayin rashin imanin shugabanin da almubazaranci.
Daga Birnin Kwanni, ga rahoton da Haruna mamman Bako ya aiko mana
Facebook Forum