Inji Ibrahim Mai Shayi yace saboda darajar Naira dake karuwa ana iya sayen kaya yau a Illelan Najeriya gobe a koma watakila dalar Amurka ta fadi, Naira ta kara daraja.
Yace kayan da aka saya yanzu an juma kadan farashin na iya sauyawa bisa ga darajar Naira saboda ba wuya a kara kudi domin wai Naira ta kara daraja. Ga masu zuwa Najaeriya daga Jamhuriyar Nijar lamarin ya rincabe masu.
A kasuwar kasa da kasa dake Illela a jihar Sokoto mai tazarar kilomita biyar kacal da birnin Konni a Jamhuriyar Nijar inda 'yan kasuwa daga sassan Najeriya da na Nijar ke halarta a kowane mako sun ce duk da farfadowar Naira sha'anin kasuwanci bai canza zani ba.
Kazalika sun kara tsunduma wajen tsadar kaya daga tarayyar Najeriya. Malam Isa yace basa jin faduwar Naira saboda kaya sun kara tsada kuma dole su kara ma nasu kayan kudi a cikin Nijar. Yin hakan kuma ya kansa mutanen gari su ga tsadar kayan.
A Najeriya darajar Naira ta tashi amma kuma 'yan kasuwan kasar basu rage farashin kayansu ba.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.
Facebook Forum