Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Rokoki Kusa Da Gidan Gwamnatin Somaliya Ya Hallaka Hallaka Mutane 7


Kananan roka da aka harba sun yi wa a kalla mutane 7 rauni kusa da fadar shugaban kasar Somalia, sa'ilin da majilisar zartasawar kasar ke gudanar da taron ta.

A kalla wadannan kananan rokokin ukku ne aka harba kusa da harabar fadar shugaban kasar. Kamar yadda direban motar daukar mara sa lafiya ya shaidawa Muryar Amurka, cewa an harba rokar ne a kusa da wani gida a yankin gundumar Wardhigley dake dab da fadar shugaban kasa, kuma farar hula hudu suka samu rauni kuma an kai su asibiti.

Sai dai rahotannin sun tabbatar cewa ba ko mutun guda daga cikin ‘yan majilisar zartaswa da wannan harin ya shafa.

An dai kai wannan harin ne sa'ilin da Firayin Minista Hassan Ali Khaire, ke tattaunawa da sabbin jami'an sabuwar gwamnati kuma babba ajandar taron ita ce yadda zasu inganta matakan tsaro a kasar da kuma yadda zasu tunkari batun fari.

Sai dai kawo yanzu ba wani wanda ya dauki alhakin aikata wannan danyen aikin.Sai dai sau tari 'yan tawayen Al-shabab, sun sha kai wa gwamnati hari.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG