Yau ne Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya karbi ziyarar Amina Ali, daya daga cikin ‘yan matan nan dari biyu na makarantar Chibok da ‘yan kungiyar Boko Haram, suka sace.
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, Ministan tsaro na Najeriya da sauran hafsoshin soji wadanda ke taka mahimmiyar rawa wurin yaki da ‘yan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, da iyayenta ne suka kasance a fadar na shugaban kasa.
Baya da aka kamala ganawar ne Malam Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari a fadar gwamnati, yace gwamnatin Najeriya, ta jajantawa Amina da iyayenta, kuma a cewar sa shugaba Buhari, yayi farin cikin gano Amina, da aka yi.
Ya kara da cewa gwamnati bazata yarda da auren dole kuma za’a tabbatar da cewa Amina ta samu kammala makaranta kuma da tabbatar da cewa ‘ya’ya mata sun sami ilimi, kamar kowa.