Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya gana da shugaban Misra a birnin Alkahira.
Bayan ganawar tasu mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen na Amurka yace sakataren ya godewa Shugaba el-Sissi saboda gagarumin goyon bayan da yake bayarwa domin ganin an samu zaman lafiya tsakanin Yahudawa da Larabawa.
To saidai mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ta Amurka Mark Toner bai kara bayani ba akan wani sabon kokari da zai kaiga sake farfado da tattaunawa tsakanin kasashen biyu wanda ya sukurkuce tun shekarar 2014 shekarar da suka gaza cimma yarjejeniya.
Ganawar ta Kerry da el-Sissi ta zo ne bayan kwana daya da shugaban Misra yace samun daidaito tsakanin Israila da Falasdinu zai taimaka wajen karfafa dangantakar kasarsa da Israila.
Shugaba el-Sissi yace samun zaman lafiya a yankin musamman tsakanin Israila da Falasdinawa zai inganta tsaro a yankin da kwanciyar hankali. Yace idan aka cimma zaman lafiya a yankin irin cigaban da za'a samu babu wanda zai yi tsammaninsa.
Firayim Ministan Israila Benjamin Natanyahu ya yabawa el-Sissi dangane da anniyarsa na son ganin an samu zaman lafiya a yankin da tsaro tsakanin kasarsa da Falasdinawa