Kungiyar likitoci na kasa da kasa tare da Gwamnatin jihar Neja, sun bude cibiyar kula da masu fama da cutar gubar dalma dake hallaka jama’a a jihar ta Neja.
Jihar Neja, na daya daga cikin jihonin da ake samun masu ginar ma’adanai na karkashin kasa ba’a kan ka’ida ba alamarin da kwararru akan fanin suka ce yana hadasa bazuwar cutar ta gubar dalma.
An dai bude cibiyar ne a yankin karamar hukumar Rafi, inda aka sami barkewar cutar gubar dalma da ta hallaka yara ashirin da takwas tare da dabbobi sama da dari a shekarar bara.
Kwamishnar lafiya na jihar Neja, Dr, Mustapha Jibril, yace hakarma’adinai da ake yi ba’a bisa ka’ida ba shine sanadiyar barkewar cutar gubar dalma wanda ke gurbata ruwa.
Ya kuma kara da cewa kungiyar agajin likitoci ta duniya wato “ Doctors without Boarders” suma sun kawo dauki.
A karkashin wanan shirin likitocin kasa da kasar har sun koyarda likitocin jihar Neja, akan yadda za’a yi saurin gano wadanda suka harbu da cutar ta gubar dalma.