Komred Sani Asha hura mai goro na cikin ‘yan kasuwar da wannan iftilain ya shafa.
‘’Ni kwance da daddare sai wani aboki na ya kira ni yace mani ga kasuwar mu ta kone da wuta musalin karfe 12;30, koda na zo abin yayi nisa kwarai, kwana-kwana sunyi iya bakin kokarin su amma lamarin yafi karfin su.Mutane sunzo domin su shigaamma jamiaan tsaro ko kuma masu gadin kasuwa su hana mmutane su shiga shi ya kawo jinkirin irin hasarar da akayi a cikin wannan kasuwa gaskiya da ace an bari an shiga tun farko da ba za ayi irin hasarar da akayi ba, masu gadin kasuwan sun hana mutane shiga ne domin kar ayi wa jamaa sata, amma da an samu shiga da hasarar ba zata kai haka ba duk da yake wasu sun tsira da wasu kayayyakin su.’’
To sai dai wakilin muryar Amurka, Murtala Faruk Sanyinna ya tambaye shi ko wane hali suke ciki yanzu ga kuma amsar da ya bashi.
‘’ALLAH kadai zai iya kawo saukin hasarar dukiyar da akayi domin batu na gaskiya kasuwar gaba ta kone domin cikin kashi 100 kashi 90 ya kone.’’
Wayewar garin gobarar tawagar gwamnatinjihar ta ziyarci kasuwar wadda take ci da wuta har lokain ziyarar jamiaan gwamnatin jihar.
Ga Murtala Faruk da ci gaban rahoton