Satar mai da fasa bututu man da ke kwarara zuwa wasu sassa kasar, na daga cikin matsalolin da ke wa arzikin Najeriya zagon kasa wajen bunkasa.
Sai dai masu fashin baki a harkokin yau da kullum sun ce, gwamnonin na Najeriya ba su da cikakken hurumin dakile wannan matsala kamar yadda jami’an tsaro ke da shi wajen kare dukiyar kasa.
“Wannan mataki zai taimaka, amma ba zai dakatar da wannan aiki na assha ba domin satar mai da ake yi ba kaiwa daga bututu ba ne ake yi ba, akwai satar mai da ake a cikin rijiyoyinmu da ke cikin teku.” A cewar Yusuf Tuga, wani masani a fannin mai.
Sai dai a cewar Tuga, inda gwamnonin za su fi taimakwa, shi ne ta hanyar samawa matasa aikin yi da sa ido a kananan hukumomi ta inda bututun mai ke ratsawa.
Baya ga satar mai a cikin gida, masanin ya ce akwai bukatar a samu hadin kan kasashe makwabta irinsu Ghana domin ana fakewa da su wajen satan man Najeriya.
Domin karin bayanin, saurari wannan cikakken rahoto na Wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa: