Wakilin Muryar Amurka, Murtala Faruk Sanyinnan, ya ruwaito cewa gidajen mai har da na mallakar gwamnati, wato NNPC ba su bude kofofinsu ba, lamarin da ya sa karancin man ya ta’azzara.
Yanzu haka masu ababan hawa na fuskantar matsala yayin da kudin sufuri ya yi tashin goron zabi a jahar ta Sokoto.
“Tun karfe shida na safe na fito nan, kusan ko wane gidan mai akwai mai, kawai dai basu so ne su sayar a farashin gwamnati shi ya sa suka rufe gidajen man.” In ji Al Mustapha Musa Fadama da ya je sayan mai.
Shi kuwa Abdulkadir Muhammed cewa shima tun da safe ya ke gidan mai, kuma idan aka zo kansu da zaran sun shiga gidan man sai ma'aikata su koro su.
“A fadawa shugaba Buhari, mu muna cikin matsalar mai, ya taimaka ma rayuwarmu.” In ji Muhammed.
Sai dai a nata bangaren kungiyar dillalan man ta kasa reshen jahar Sokoto ta ce matsalar na da alaka da bacin hanyar Ilori inda ta nan ne ake bi da man.