Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Na Neman A Kwashe Ma'aikatan Jakadanci


Motar sojan Koriya ta Arewa dauke da wani makami mai linzami lokacin fareti a dandalin Kim Il Sung a Pyongyang.
Motar sojan Koriya ta Arewa dauke da wani makami mai linzami lokacin fareti a dandalin Kim Il Sung a Pyongyang.

Wani jami'in ofishin jakadancin Rasha yace an ba su takardar shawarar kwashe ma'aikatansu a saboda zaman dar-dar dake karuwa a yankin na Koriya

Wani jami’in ofishin jakadancin kasar Rasha a Pyongyang, babban birnin Koriya ta Arewa, yace hukumomin kasar sun shawarci Rasha da ta kwashe ma’aikatan ofishin nata a saboda zaman dar-dar dake karuwa na yankin kasashen na koriya.

Jami’in mai suna Denis Samsonov, ya fada yau jumma’a cewa Rasha tana nazarin wannan bukata, amma a yanzu ba ta da wani shiri na kwashe ma’aikatanta. Yace a halin yanzun, babu wata lamar tashin hankali a birnin Pyongyang.

Samsonov yace sauran ofisoshin jakadancin kasashen waje dake Pyongyang su ma sun samu irin wannan takarda.

A cikin ‘yan makonnin nan, Koriya ta Arewa ta yi ta aikewa da barazana ga Amurka da Koriya ta Kudu, ciki har da barazanar kai harin nukiliya a kan Amurka.

A halin da ake ciki, wani jami’in Koriya ta Kudu yace watakila Seoul zata janye ma’aikatan kasarta daga wata cibiyar masana’antu ta hadin guiwa dake cikin Koriya ta Arewa, idan har suka shiga cikin hatsari. Ministan sake hade kasashen Koriya na Koriya ta Kudu, Ryoo Kihl-jae ya fada yau jumma’a cewa a yanzu dai ma’aikatan ‘yan kasarsa ba su cikin mummunan hadari.

Wannan cibiyar masan’antu ta kaesong tana daya daga cikin abubuwa kalilan da suka hada kasashen biyu, kuma ita ce babbar hanyar samun kudaden musanya na waje ga kasar Koriya ta Arewa.
XS
SM
MD
LG