WASHINGTON, D.C - A yau Alhamis ne Ma'aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa din take cewa Koriya ta Arewa zata yi abinda yake hakkinta na soma daukar matakin kaddamarda harin nukiliya akan abinda ta kira “hedkwatar mai tsangwamarta.”
Tace daukar wannan matakin ya zama wajibi a kanta tunda “Amurka na neman kyasta ashanar soma yakin nukiliya.”
Koda yake an san cewa Koriya ta Arewa tayi nisa sosaio wajen kokarin da take na mallakar makaman kare dangi na nukiliya, ana jin har yanzu bata kai inda take da fasahar da zata iya cinna makamai masu linzame da za’a makalla kundajin nukiliya din ba.
Amma sau da yawa, duk lokacinda aka shiga halin zaman dar-dar, akan ji ta tana irin wannan barazanar cewa ata iya.
Wannan barazanar ta yanzu tana zuwa ne ana sa’oi kalilan kafin Majalisar Dinkin Duniya ta yanke shawarar daukar wasu sababbin matakan da akace sune mafi gauni na karya Koriya ta Arewa din.