Taron kolin Majalisar Dinkin Duniyar, wanda shine matakin karshe a tsarin diflomasiya, na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Lebanon suka bayyana cewar hare-haren da Isra’ila ke kaiwa sun hallaka mutane 560 daga cikinsu yara kanana.
Ministan Tsaron Najeriya Abubakar Badaru ne ya gabatar da bukatar a taron kolin da aka yi kan makomar duniya yayin karo na 79 na babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya dake gudana a birnin New York, na Amurka.