Shugaba Joe Biden na cigaba da fuskantar kadaici a zahiri da kuma a siyasance, inda ya ke fama da cutar COVID 19, a daidai lokacin da ake tsaka da yakin neman zabe, da karin kiraye kiraye daga 'yan Democtar na ganin ya janye da ga tsayawa takara tsakanin shi da tsohon Shugaba Donald Trump.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Republican J.D. Vance ya yi jawabi a dare na uku na babban taron jam'iyyar Republican jiya Laraba. Abokin takarar na Donald Trump ya rungumi tsarin " Sa Amurka kan gaba" dangane da manufofin kasashen waje, da kuma tsaro.
Fadar gwamnatin Amurka ta white House ta sanar cewa, Shugaba Joe Biden ya kamu da cutar COVID 19 a ranar Laraban nan, jim kadan bayan ya soke gabatar da jawabi a Las Vegas inda ya shirya zai janyo hankalin al'ummar Latino masu kada kuri’a.
Kwana na 3 na babban taron jam’iyyar Republican zai soma a daren yau Laraba karkashin jagoranci hadakar Donald Trump da JD Vance da aka zaba a baya-bayan nan zasu maida hankalinsu kan batutuwan da suka shafi tsaron kasa da manufofin kasashen ketare.
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana jiya Litinin cewa, ya yi kuskure lokacin da ya gaya wa magoya bayansa cewa su “auna” abokin hamayyarsa Donald Trump a kokarinsa na jan hankali kan halayen abokin hamayyarsa, amma ya ce Trump yana yin amfani da kalamai masu tayar da hankali a kai a kai .
Trump mai shekaru 78 ya zabi Vance mai shekaru 39 a matsayin abokin tafiyarsa a takarar shugaban kasa a watan Nuwamban 2024.
Daga cikin mutane uku da ake sa ran Trump zai zaba a matsayin mataimaki, akwai Sanata J.D. Vance na jihar Ohio, Sanata Marco Rubio na jihar Florida da gwamnan North Dakota Doug Burgum.
Hukuncin na zuwa ne kwana biyu bayan da Trump ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wani dan bindiga ya yi yunkurin halaka shi.
Wani abokin karatun Thomas Matthew Crooks, matumin da ake zargi da yunkurin kashe Trump, ya bayyana shi a matsayin wanda aka tsangwama, ba mai hulda da shi sosai, yayin da masu bincike suka gano ababen fashewa a cikin motar Crooks da gidansa.
Sakataren tsaron cikin gida na Amurka, Alejandro N. Mayorkas ya fitar da wata sanarwa game da harbin da aka yi a wurin yakin neman zaben tsohon Shugaban kasar Donald Trump a jihar Pennsylvania da safiyar yau.
Ofishin yakin neman zaben tsohon Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa, tsohon Shugaban kasar ya samu rauni a ka yau Asabar, amma yana “lafiya” bayan da aka harba bindiga a wajen da ya ke wani gangamin yakin neman zabe a Pennsylvania.
Alamu na nuna an harbi dan takarar jam'iyyar Republican kuma tsohon shugaban Amurka Donald Trump a wani taron yakin neman zabe a garin Butler da ke jihar Pennsylvania a Amurka ranar Asabar.
Domin Kari