An kama tsohon mai taimaka wa Donald Trump kan harkokin siyasa, Steve Bannon a jiya Litinin bayan da ya kai kansa ga hukumomi a gidan yarin tarayya saboda kin amsa sammacin da Majalisar Wakilai ta yi masa lokacin da take gudanar da bincike kan tashin hankalin da aka yi a ranar 6 ga Janairu, 2021.
Kotun kolin ta yanke hukunci jiya Litinin cewa, shugabannin Amurka suna da kariya daga tuhuma kan laifukan da suka aikata lokacin da suke kan karagar mulki, kuma suna da cikakkiyar kariya daga gurfanar da su a gaban kotu a kan abinda su ka aikata yayinda su ke gudanar da aikin Shugaban kasa.
Amurkawa sun bayyana batutuwa da su ke da muhimmanci a zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Nuwamba da suke neman amsa a muhawarar da 'yan takarar Shugaban kasa suka fafata karon farko a kakar zaben bana.
Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban kasar Donald Trump sun gwabza muhawara a daren Alhamis, inda suka fafata kan tattalin arzikin Amurka da harkokin kasashen waje da hakkin zubar da ciki da kuma batun kaura daga kan iyakar Mexico zuwa Amurka.