Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta samu goyon bayan wadatattun wakilan jam’iyyar Democrats domin zama wacce zata kara da Donald Trump 'dan Republican, a cewar binciken da kamfanin dillancin labarai na AP ya gudanar, kasancewar jiga-jigan ‘yan Democrats na mara mata baya.
A jiya Litinin ‘yan majalisar dokokin Amurka daga bangarorin biyu suka yi kira ga Daraktar hukumar tsaron farin kaya ta Amurka Kimberly Cheatle da ta yi murabus, yayin da take ba da shaida kan gazawar hukumar wajen hana yunkurin kashe dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donald Trump.
Masu fashin baki akan tafiyar siyasar duniya sun bi sahun sauran al'umma wajen bayyana matsayinsu dangane da matakin Shugaba Joe Biden na janye takararsa daga zaben Shugaban kasa na watan Nuwamban 2024.
Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta kaddamar da yakin neman zabenta na 2024, inda ta nemi goyon bayan 'yan jam'iyyar Democrat tare da neman hadin kan Shugaba Joe Biden wanda ya janye daga takarar sakamakon nuna damuwa da aka yi kan shekarunsa da lafiyarsa.
Membobin jam'iyyar da dama sun ce suna goyon bayan Harris a matsayin wacce zata maye gurbin Biden a jam'iyyar kuma wacce za tayi takarar shugabancin kasar tare da Trump. Sai dai wasu sun ce suna bukatar jam'iyyar Democrat ta yi zabben fidda da gwani a babban taron jam'iyyar na wata mai zuwa.
Shugabannin duniya sun fara bayyana ra’ayoyin su bayan shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da janyewa daga takarar shugabancin kasar a jiya Lahadi.
Kusoshin jam’iyar Democrats da su ka hada da tsohon Shugaban kasa Barak Obama, da tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi sun yabi Shugaban kasa Joe Biden domin janyewa daga takarar Shugaban kasa a zaben da za a gudanar a watan Nuwamba
‘Yan Democrat na bayyana damuwa game da yadda masu kada kuri’a ke jefa ayar tambaya kan shekarun Biden da kuma damar samun galaba kan Trump a zabe mai zuwa idan ba a yi wani babban sauyi ba.
Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya shiga tsaka mai wuya kan yadda zai shiga tsakani dangane da kiraye-kirayen da ake yi wa Shugaba Joe Biden na ya janye takararsa.
Jam'iyar Republican ta tsayar da tsohon Shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin dan takararta a zaben Shugaban kasar da za a gudanar a watan Nuwamba wannan shekarar.
Domin Kari