Kwamitin harkokin siyasar da musk ya kafa a Amurka (PAC) ya tarawa yakin neman zaben trump dala miliyan 74.95 a tsakanin 1 ga watan Yuli da 30 ga watan Satumbar da ya gabata, a cewar bayanan hukumar zaben tarayyar kasar.
A duk bayan shekara hudu, fafutukar lashe zaben shugaban kasar Amurka ta na fin raja’a ne a muhimman jihohin raba-gardama.
Fafatawar Walz da Vance zai kasance a yau Talata 1 ga watan Oktoba da karfe 9 na dare agogon ET da Laraba 2 ga watan Oktoban da muke ciki da karfe 1 na safe agogon UTC.
Miliyoyin Amurkawa ne suka kali wannan muhawara da watakila za ta kasance daya tilo a wannan lokacin yakin neman zabe.
Alamu sun nuna cewa Biden ya dan zubar da hawaye a lokacin da ya hau dandamalin da ya yi jawabin inda aka kwashe sama da minti hudu ana sowa da nuna masa kyakkyawar tarba.
Jiga jigan 'yan jam'iyyar Democrat sun fara jawabai a babban taron jam'iyyar da za a shafe wajen mako guda ana yi a birnin Chicago na jahar Illinois ta nan Amurka.
Fitowa da yin jawabi ba zato ba tsammani da Mataimakiyar Shugaban Amurka kuma 'yar takarar shugaban kasa, Kamala Harris, ta yi a babban taron jam'iyyar Democrat na daya daga cikin jerin abubuwan da su ka burge jama'a a daren farko na taron na kusan mako guda.
Jam’iyyar Democrat ta fara babban taronta na kasa a ranar Litinin a Chicago inda ake sa ran kusan mutum 50,000 za su isa birnin.
Kamfanin manhajar Google ya ce wata kungiyar kasar Iran mai alaka da Dogarawan Juyin Juya Halin kasar, ta yi ta yinkurin yin kutse ga akwatin sakonnin intanet na mutane wajen 12, wadanda ke da alaka da Shugaban Amurka Joe Biden, da tsohon Shugaba Donald Trump, tun daga watan Mayu.
An sake zaben Walz a wa’adi na biyu a shekarar 2022 a jihar ta Minessota bayan da ya doke dan takarar jam'iyyar Republican Scott Jensen.
Walz, wanda Gwamna ne mai ci kuma tsohon soja, ya taka muhimmiyar rawa wajen kare ‘yancin zubar da ciki a Amurka.
Domin Kari