‘Yan kasuwa a Maiduguri babban birnin jihar Borno sun tafka asara ta miliyoyin naira sakamakon mummunar gobata da ta kone babbar kasuwar Maiduguri kurmus.
Yayin da miliyoyin mutane a Najeriya ke kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a ranar Asabar din nan, Muryar Amurka ta tattauna da jami’an hukumar zabe, da masu sa ‘ido a game da muhimman abubuwa a kan zaben.
INEC ta ce ta shirya tsaf don gudanar da zabe, yayin da hukumomin tsaro suka ce sun yi kyakkyawan tanadi don ganin zaben ya gudana lami lafiya. Sai dai zaben na bana, ya zo a daidai lokacin da jama’a ke fama da karancin kudi, sakamakon sabon tsarin canjin kudi, da wasu rahotanni
A Ghana ma, akwai ‘yan Najeriya da dama dake gudanar da sana’o’i. A birnin Kumasi, wasu ‘yan Najeriyar da ba su iya komawa kasarsu yin zaben ba saboda matsalar tsaro da kuma karancin sabbin kudi, sun koka da yadda babu wani tsari da zai ba ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje damar yin zabe.
Anas Muhammad Sani, wani dan Najeriya ne dake karatu a Ingila wanda ya yi tafiyar mil 3,200 zuwa Najeriya tare da iyalansa domin yin zabe. Alhassan Bala a Abuja ya tambaye shi dalilin da ya sa ba za a yi wannan zabe ba da shi ba.
Sai dai zaben na bana, ya zo ne a daidai lokacin da jama’a kef ama da karancin kudi – sakamakon sabon tsarin canjin kudi da aka bullo da shi a kasar. Karancin sabbin takardun naira din dai ya shafi shirye-shiryen mutane, da ‘yan siyasa na gudanar da zaben.
A Nijar mai makwaftaka da Najeriyar akwai ‘yan Najeriya da dama da suke gudanar da sana’o’insu a can inda suke zama tare da iyalansu. Wasunsu sun yi shirin komawa kasarsu domin ganin an dama da su a wannan zabe. Amma akwai wasu da suka ce ba su ga wani dalili da za isa su zuwa Najeriya yin zaben ba.
Duk da cewa mutane a Maiduguri babban birnin Jihar Borno sun fito da dama domin INEC ta gudaanar da Zaben gwaji, an samu tangardar na’urar BVAS a wasu wurare, amma Jami’in Zabe Aliyu Abubakar ya ce shafa lalle da lalacewar yatsu kan kawo hakan.
Wasu ‘yan takara, har kasashen waje suke fita domin haduwa da ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen waje. A makon da ya gabata ne Peter Obi, wanda ke takara a jam’iyyar Labour ya je Amurka inda ya hadu da ‘yan Najeriya a wasu birane, ciki har da Washington DC.(An buga asali a ranar 9 ga Satumba, 2022)
Mun duba yadda a wannan makon gwamman babban bankin Najeriya ya ce wa’adin 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsofaffin manyan takardun naira ya na nan daram, lamarin da ya sa murna ta koma ciki a wajen mutane da dama da suka yaba da matakin kotun kolin kasar daga farko.
A Jamhuriyar Nijar wata mata ta dukufa taimakawa marayu da sauran yara da ake yarwa bayan an haifesu. Matar ta ce tana yin wannan aikin sa kai ne don baiwa irin wadanan yara samun rayuwa kamar ta kowa, da wasu rahotanni
Domin Kari