Yayin da Pepe ke zargin Alkalin wasa da taka rawa wajen rashin nasara da Portugal ta yi, shi kuma Cristiano Ronald, zubar da hawaye ya yi ta yi sharbe sharbe.
Morocco ta kafa tarihi na zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya, bayan da ta ci Portugal 1-0 a wasan Quarterfinals.
Croatia ta yi nasara akan Brazil ne a bugun fenariti bayan da aka tashi da ci 1-1-
Kasar Morocco ta dan ceci nahiyar Afurka da duniyar Larabawa daga kunya, bayan da ta kasance daya tilo da ta rage a gumurzun kwallon kafa da ake gwabzawa a kasar Qatar.
A daya daga cikin wasanni masu jan hankali a gasar cin kofin duniya ta bana, kasar Netherlands ta kirba Amurka 3-1.
Ita dai Koriya ta Kudu ta shammaci Portugal ne ta zura mata wata makararriyar kwallo, wacce ita ta tilastawa Uruguay ficewa.
Ita dai Australia ta doke Denmark ita ma da ci 1-0 a rukunin na D, hakan ya ba ta damar karbe matsayi na biyu a teburin rukunin da yawan kwallaye.
nasara a wannan wasa ne kadai za ta ba Argentina damar zuwa matakin gaba a gasar yayin da kunanen doki zai iya sa ta shiga zagayen, amma hakan ya danganta ne da yadda sakamakon daya wasan rukunin zai kaya.
Ghana dai ta gaza cin wasanta na farko da Portugal a farkon bude gasar wacce ake yi a Qatar.
Domin Kari