'Yar kasar Rwanda Salima Rhadia Mukansanga ta zama mace ta farko da ta yi alkalancin wasan Guinea-Zimbabwe a gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Kididdigar hukumar kwallon kafa ta FIFA ta 2021 ta nuna cewa Ghana ce kasa ta 52 da ta iya taka leda a duniya yayin da Comoros ke matsayin 132.
A wasanta na farko, Ghana ta sha kaye a hannun Morocco da ci 1-0 yayin da ta yi kunnen doki da ci 1-1 da The Panthers of Gabon a ranar Juma’a.
Tuni Kamaru ta tsallaka zuwa zagayen 'yan 16 da za a fara sallamar duk kasar da aka ci.
A ranar Laraba Najeriya za ta kara da Guinea-Bissau duk da cewa ta shiga zagaye na gaba yayin da Sudan za ta fafata da Masar.
Kamaru dai ta ci wasanninta biyu, inda ta doke Burkina Faso a wasanta na farko a rukuninsu na A.
Yayin da Mali ke kan gaba da ci daya mai ban haushi, alkalin wasan Janny Sikazwe dan kasar Zambia ya hura karshen wasan a karon farko a minti na 85.
Domin Kari