Wane irin kalubale ake fuskanta wajen yin hoton X-ray a al’ummar ku? Shin kun taba damuwa a game da ingancin X-ray da sauran nau’ukan hoto don kula da lafiyarku? Ga abinda wasu ‘yan Najeriya suke cewa.
Dr. Aliyu Suleiman, Kwararre a fannin hoton xray a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna, ya yi bayani a game da mahimmancin hoton X-ray da wasu kalubalolin da ake fuskanta a nahiyar Afirka da mafita.
Fasahar daukan hoton xray a fannin kula da lafiya ta na taka mahimmiyar rawa wajen magance cututtuka. Hoton xray - Ultrasound ko kuma CT scan na daga cikin jerin fasahohin da likitoci suke dogaro da su wajen ganin cikin jikin dan Adam don gano irin cuta, sa ido ko yin maganin cututtuka.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta amince da wani sabon nau’in maganin rigakafin kwalara da ake digawa a baki.
An gudanar da gasar lig ta wasan kwallon Kwando da Olympics ta musamman ta nahiyar Afirka a Dakar, babban birnin kasar Senegal, da wasu rahotanni
Mashahurin mawakin na Afrobeat Davido, ya rattaba hannun yarjejeniya da kamfanin rarrabawa da kasuwancin wakoki na Amurka, da wasu rahotanni
Domin Kari