Masu sa ido sun ce breast ironing wani nau’in cin zarafin yaya mata ne da ke janyo radadi mai tsanani, lalata hallita, wanda ke kaiga kamuwa da cututtuka da kuma dimuwa. Galibi wannan al’ada ce da aka santa a nahiyar Afirka inda mata akalla miliyan 3.8 suke fuskanta a tsakanin Kamaru da Najeriya.
Mun nemi jin ta bakin wasu a jihar Kaduna kan wannan ta’adar dakile girman nono ‘ya mace da kuma abin da ya kamata a yi don kawo karshenta. Ga abin da suka sheda mana
Dr. Yunus Babeeb Yunus, wani babban likita ne a asbitin kwararru na jihar Borno dake Maiduguri, ya yi bayani a game da haduran da ke tattare da wannan al’adar dakile girman nono ‘ya mace da abubuwan da suka dace ayi don taimakawa wadanda suka fuskance ta.
Domin Kari