Me kuke fatan ingantawa ko cimma a shekarar 2023? Ga wasu daga cikin ra’ayoyin ‘yan Najeriya akan wannan.
Dr. Fatima Anga, Likita a asibitin gwamnatin tarayya dake Jabi-Abuja ta yi mana bayani a kan abubuwan da ya kamata mutane su yi don kula da lafiyarsu a wannan sabuwar shekarar milladiya.
Ma'aikatar lafiya ta kasar Kenya ta ce ayyukan wayar da kai ta fasahar zamani kan ilimin saduwa da aka kaddamar don taimakawa wajen shawo kan matsalar daukan ciki a tsakanin ‘yan mata da basu manyanta ba a kasar ya samu matasa fiye da dubu 5 a yanzu.
Prostate wani sashin al’aura ne da ake samu a marar maza kawai. Wannan sashi na gaban maza na fitar da wani ruwan da ke cikin maniyyi. Ƙungiyar kula da cutar daji ta kasar Amurka ta ce ana samun cutar daji na gaban maza ne a lokacin da ƙwayoyin sashen gaban suka fara yin girma fiye da kima.
Dakta Abdulsalam Kayode Shuaibu mataimakin darakta a sashen Kula da lafiyar 'yan wasa a ma'aikatar matasa da wasanni ta Najeriya ya yi bayani a kan yadda ya kamata mutanen da ke fama da wasu rashin lafiya da su rika taka-tsantsan da yanayin sosawar zuciyar su yayin kallon gasar wasanni kamar gasar.
Ta yaya mutane ke murna idan kungiyoyin da suke goyon baya suka sami nasarar ko kuma rashin nasara, kuma shin hakan zai iya shafar lafiyarsu da jin daɗinsu? Ga ra’ayoyin wasu a Kano.
Masana sun ce rashin nasarar wata kungiyar kwallon kafa a lokacin wasannin na da nasaba da yawaitar yunkurin kashe kai da ake yi da kuma shiga damuwa ko tunani da dai sauransu.
Mun nemi jin ra'ayinku a kan yadda ake magance bullar cutar kyandar biri a halin yanzu, kuma menene ku ke son ku gani na daban a yanayin daukar matakai a game da cutar? Ga ra’ayoyin wasu mazauna birnin Jos, na Najeriya.
Ga wasu irin kalubalen da wata mace a kasar Mozambique da ta yi fama da cutar tundurmi ta ke fuskanta.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.
Domin Kari