Bayan wanke tsohon shugaban kasar Donald Trump da majalisar dattijai ta yi akan zargin tunzura magoya bayansa tayar da tarzoma a ginin majalisar, ba bu tabbas a game da makomar Trump din a siyasance.
Masu sharhi kan harkokin yau da kullun a Najeriya na ci gaba da tsokaci a game da irin aikin dake gaban sabbin manyan hafsoshin tsaron kasar da suka kama aiki kwanan nan. Dr. Umar Goni, Malami a Jami'ar Maiduguri, ya ce ‘yan Najeriya su na sa ran ganin babban canji cikin kankanin lokaci.
Ku leka jihar Katsina a Arewacin Najeriya don ganin wani sabon yunkuri da hukumomi ke yi na yaki da matsalar tsaro.
A Ghana, fim din Da Yie wato Good Night, da ya bada labarin wasu yara biyu da wani bako ya kai su wani balaguro na sauya rayuwa ya samu lambar yabo ta Oscar.