Ali Nuhu fitaccen jarumin fina-finan Hausa a Najeriya, wanda fina-finansa suke samun karbuwa a ciki da wajen kasar ya shaida mana irin kalubalen da ya fuskanta a harkar, da kuma kokarin da suke yi na ganin fina-finan Hausa sun samu karbuwa a Netflix.
Sana’ar kiwon tsuntsaye, ta na ci gaba da kara karbuwa a tsakanin matasa a yankin Maradi na jamhuriyar Nijar. Matasan suna samun makudan kudade daga siyar da tsuntsayen, wasu tsuntsayen ma daga kasashen waje suke shiga Nijar din da su.
Bisa ga dukkan alamu dai, shugaban Rasha Vladimir Putin bai yi tsammanin girman takunkumin da kasarshi za ta fuskanta sakamakon kaddamar da yaki a Ukraine, zai kai yadda abin ya kasance a yanzu ba.
Labarin wani matashi mai basirar hada motoci masu amfani da lantarki a jihar Bornon Najeriya, wadanda ya ce za su saukake harkar sufuri da dumamar yanayi a kasar.
Ofisoshin jakadancin Najeriya a Poland da Hungary da Romania suna ci gaba da karbar ‘yan Najeriya dake tahowa daga Ukraine domin kai su gida. Dr. Safiya Ahmed Nuhu, jakadiyar Najeriya a Romania ta yiwa Muryar Amurka karin bayani kan yadda aikin ke tafiya.
Bayan wasu korafe-korafe daga wasu ‘yan kasar, shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya shaidawa Muryar Amurka dalilin da yasa kasarsa ta amince ta karbi sojojin Faransa da ke janyewa daga Mali.
Hira ta mussaman da gwamnar jihar Filato Simon Lalong akan matsalolin da Jam'iyyar APC mai Mulki ke cigaba da fuskanta gabanin taronta.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC ya ce ko kadan babu siyasa ko bita da kulli, a binciken da suke gudanarwa kan wasu tsofaffin gwamnoni a kasar.
Mun tattauna da Dakta Aminu Yushua Ibrahim a game da halin da yara da manya suke iya shiga bayan cin zarafin da Malaman makaranta sukayi masu da kuma illar tsare su a wadannan cibiyoyi.
Mun samu ji daga bakin daya daga cikin daliban makarantar mari da aka gano a jihar Kano, inda ake zargin malaminsu da cin zarafin dalibai.
Hukumomin Kenya sun bullo da tukwici na ba makiyaya magunguna ga dabbobinsu na lalurorin yau da kullun, domin karfafa gwiwarsu su karbi allurar rigakafin COVDI-19.
Wani kamfanin hadin gwiwa na Sweden da Kenya, mai suna Opibus, ya kaddamar da wata motar bas ta farko da aka kera mai amfani da lantarki a Kenya.
Domin Kari