Hukumomi a Nijar sun tashi tsaye don kwashe ‘yan kasar dake barace-barace a titunan wasu kasashen Afirka, saboda bata sunan Nijar din da suke yi.
To kafin gwamnatin Nijar ta fara kwashe ‘yan kasarta dake bara a Ghana, wasu shugabannin al’umma a birnin Kumasi na Ghana sun yi ta kokawa a game da matsalolin da mabaratan a tituna ke haifarwa.
Kasashen duniya na ci gaba da sa ido sosai akan yawaitar matsalar harbi da bindiga a Amurka, kwatankwacin wanda ya faru a Uvalde naTexas. Amurkawa da basu ji ba basu gani ba, musanman yara na ci gaba da rasa rayukansu sakamakon bude wuta da mutane keyi da bindiga.
Za mu fara Shirin ne daga jamhuriyar Nijar inda hukumomi suka bude wata sabuwar cibiya ta gyaran halin ‘yan ta’adda da suka tuba a Hamdallaye da ke yankin Tillaberi, domin ci gaba da ba ‘yan ta’adda damar mika wuya.
Yayin da shirye-shiryen babban zaben 2023 a Najeriya ke ci gaba da kankama, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben. Atiku Abubakar dai ya sha yunkurin zama shugaban Najeriya a baya, ba tare da nasara ba.
Masana harkokin tsaro a Kano dake arewa maso yammacin Najeriya sun yi gargadin cewa kwararowar mabarata cikin jihar daga jihohin makwabta da ke fama da matsalar tsaro, wata babbar barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Mutane da dama da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a jihar Bornon Najeriya na ci gaba da samun kubuta yayin da sojoji ke ci gaba da yiwa ‘yan ta’addan lugudan wuta. Wasu mutane biyu da suka samu kubuta a baya-bayan nan sun bayyana wa.
Game da tasirin ricikin na Ukraine akan tattalin arzikin kasashen duniya, Muryar Amurka ta tattaunawa da masana tattalin arziki daga kasashen Afirka da ban daban.
Hafsa wacce take sana’ar yin lalle na zamani, da gyaran gashi da kuma fata da ke kira Henna ta Hafsatee, ba kawai ta na nuna yadda mata za su iya zama masu dogaro da kansu ba ne, har ma su kasancewarsu masu daukar wasu aiki.
Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500 daga hannun mutane a jihar Filato cikin shekaru biyu, a wani mataki na yaki da matsalar tsaro a kasar.
Jihohi da dama a arewacin Najeriya na fama da matsanancin yanayin zafi, inda har yakan kai maki 35 zuwa 40 na ma’aunin celcius a wasu wuraren. Musulmai da suke gudanar da azumin Ramadan na bana a yankunan da ke fama da yanayin na zafi suna yin azumin da wuya.
Domin Kari