A shekarar 1984, gwamnatin soji karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta sauya kudin Najeriya, a wani mataki na yaki da cin hanci da rashawa. Sai dai karancin lokaci da aka ba jama’a na su sauya kudadensu, ya sa da dama yin babbar asara. Shin ko a wannan karo an koyi darasi daga lamarin na 1984?