Hukumomi a Jamhuriyar Nijar tare da hadin gwiwar kungiyar ECOWAS, EU da Majalisar Dinkin Duniya, sun fara wani aikin karbe makamai da mutane ke rike da su ba bisa ka’ida ba a fadin kasar.
Bayan shiru na wasu kwanaki tun bayan hukuncin kotun kolin kasar, babban bankin Najeriya ya umurci bankuna a kasar da su ci gaba da mu’amala da tsofaffin takardun kudi na naira 200, da 500 da dubu daya har zuwa karshen wannan shekara.
Hukumomin lafiya a Ghana sun fara kai allurar rigakafin cutar kyanda a cibiyoyin kiwon lafiya domin shawo kan barkewar cutar da ya zuwa yanzu ta kama mutane 120.
Dr. Sa'adou Habou, likitan kwakwalwar a sashen dake kula da masu tabin hankali a babban asibitin Maradi, ya yi mana karin bayani a game da lalurar ta’ammali da miyagun kwayoyi.
An bullo da wata sabuwar fasahar aikin likita inda ake amfani da na’urar VR wajen taimakawa marasa lafiya samun saukin radadi mai zafi sosai da kawar da damuwa, da ma taimakawa wajen haihuwa.
A cewar wani sabon binciken da aka buga a mujallar Lancet, tsakanin kaso 38-50 cikin 100 na marasa lafiya dake fama da cutar kyandar biri wato mpox na duniya suma suna fama da cuta mai karya garkuwar jiki.
Wata cibiyar kula da wadanda suka yi fama da tu’amalli da miyagun kwayoyi a birnin Maputo tana taimaka wa wadanda suka daina shaye-shaye su ɗauki matakan farko na murmurewa daga matsalar.
Wata malamar makaranta a Kumasi, Ghana ta na taimakawa wajen magance matsalar rashin zuwa ‘ya’ya mata makaranta, ta hanyar samar mu su da audugar mata da za ta taimaka mu su yayin da suke al’ada.
Domin ganin kasar ta iya show kan kalubalen shirya bikin baje kolin fina-finai na FESPACO karo na 28 da yanayin tabarbarewar tsaro ya yi mummunan tasiri akai, gwamnati Burkina Faso ta sa hannu sosai a cikin wasu fina-finai da ake yi a kasar.
China ta soki matakin da gwamnatin Biden ta dauka na amincewa da cinikin dala miliyan 619 na sayar wa Taiwan makamai wanda ya hada da daruruwan makamai masu linzami na jiragen yakin F-16.
Munji ta bakin Farfesa Ghali Sadiq na jami’ar Abuja, mai sharhi ne kan al’amuran siyasa a Najeriya, akan yadda yake kallon wannan takaddama ta zaben shugaban kasa.
Biyo bayan korafe-korafe da dama na rashin bin wasu ka’idoji wajen gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, hukumar zaben kasar INEC ta ce ta na daukan matakan gyara domin tabbatar da cewa ba a gamu da wata matsala ba a zaben gwamnoni.
Domin Kari