Kananan manoma mata a yankunan karkarar dake Nijar sun ce rashin samun muhimman abubuwan noma kamar ingantaccen iri da taki na hana su fadada ayyukansu na gona.
A wata hira a Ghana Abubakar Siddiq Ali yana daga cikin wadanda suke da iyali a Sudan, kuma rikicin kasar ya hana su samun yin magana da iyalin akai-akai.
Sannu a hankali zamani ya sa an fara mantawa da wasan hawan kaho, daya daga cikin al’adun kasar Jamhuriyar Nijar da mutane ke alfahari da su shekara da shekaru.
Malam Kabir Adamu, masanin al’amuran tsaro a Afirka dake Najeriya ya yi mana karin haske akan yadda rikicin Sudan zai shafi sha’anin tsaro a sauran kasashen Afirka, da kuma yadda za a kawo karshen wannan rikici.
Amurka da sauran kasashen duniya sun yi ta kwashe ‘yan kasarsu dake Sudan, musanman ma’aikatan diflomasiya, yayin da rikicin tsakanin sojoji da runsunar RSF ke kara tabarbarewa.
Rikicin a wasu sassan Sudan ya ritsa da fararen hula da dama a Khartoum babban birnin kasar.
Manazarta na cewa musabbabin wannan rikici na Sudan zai yi mummunan tasiri a kasar. Ko me ya canja tsakanin bangarorin biyu?
Najeriya ma ta bi sahun kasashen duniya da suke kokarin kwashe ‘yan kasarsu da suka makale a Sudan, musanman dalibai. Sai dai aikin kwashe mutanen ya na cike da kalubale saboda babu damar amfani da jirgin sama daga Khartoum.
A daren Talata bangarorin Sudan biyu dake gwabza fada suka fara aiki da wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’o’I 72 da Amurka da Saudiya suka jagoranci cimmawa. Sai dai duk da yarjejeniyar, an ci gaba da samun ‘yan hare-hare anan da can.
A birnin Maiduguri dake Najeriya, ‘yan kasuwar Monday Market da ta yi gobara a watannin baya, sun nuna rashin jin ‘dadinsu a game da yadda sallar bana ta zo musu.
Tsadar filawar alkama wacce ta haifar da tashin farashin biredi a Ghana, ta sa wasu masu sana’ar biredin komawa amfani da rogo da ake nomawa a kasar.
Yadda bayan azumin bana ya kai karshe, musulmai a Jamhuriyar Nijar suka yi shirin gudanar da bukukuwan sallah, musanman a ranakun karshe.
Domin Kari