To Ghana ma, a lokacin da suka yi shirye-shiryen shagulgulan karamar sallah, mutane sun koka kan tsadar kaji, abin da wasu suka ce zai hana su morewa bikin kamar yadda suka saba a kowace shekara.
Ga mutane da yawa a Amurka, bukukuwan hutu na nufin sanya kayan ado a harabar gidaje. Yanzu, wasu iyalai Musulmai sun samo hanyoyi na musamman na bayyana bikin watan Ramadan.
Wani mutum a Ghana, Mustapha Ibrahim yana tsaftace muhalli ta hanyar karba tare da sarrafa robobi zuwa man fetur da man gas.
Cibiyar binciken amfanin gona a Ghana ta fara horas da manoman Tumatir kan yadda ake sarrafa tumatur ya zama tumatirin gwangwani wato Jam da fatan wannan shiri zai kasance mai dorewa kuma tushen samun kudin shiga.
A nan Amurka, yunkurin hana yara shiga kafafen sada zumunta a hukumance na kara yin zafi. Ya zuwa yanzu, masu bincike sun ce akwai abubuwa da dama marasa kyau da kuma nagartattu wanda kananan yara zasu iya cin karo da su a dandali.
Zababben gwamnan jihar Filato a Arewcin Najeriya, Barista Caleb Mutfwang na jam'iyyar adawa ta PDP, ya sha alwashin tabbatar da adalci a tsakanin al'ummar jihar da ke fama da rikicin kabilanci da na addini.
A lokacin da alaka ta fahimta tsakanin mabiya addinai a Najeriya ke kara tabarbarewa, wani bawan Allah kirista dan Kabilar Igbo ya kai gudummawar butoci ga makwabtan sa musulmi domin su samu saukin yin ibada a wata mai Alfarma na Ramadan.
A Jamhuriyyar Nijar masu sana’ar kamun kifi da masu noman rani a babban tafkin Madarumfa dake cikin yankin Maradi a gabas maso tsakiyar kasar, sun nuna damuwarsu game da yadda ruwan wannan tafkin ke ci gaba da janyewa.
Wata kungiya mai suna "Femmes en Marche" tana aiki tare da kungiyoyin kasa da kasa wadanda ke kokarin taimaka wa iyalai da ke tserewa daga Burkina Faso.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da azumin watan Ramadan, Malamai na ci gaba da jan hankali akan muhimmancin wannan wata da falalarsa.
Yadda a Najeriya aka gurfanar da wasu sojoji a gaban kotun soji, da ake tuhumar su da aikata laifukan da suka hada da take hakkin fararen hula.
Gasar Lig ta kwallon kwando ta Afirka da aka fara tun shekarar 2019, wani sashe ne na hukumar kwallon kwando ta Amurka wato NBA, da ke fadada lamurran wasan kwallon kwando a nahiyar Afirka, wanda aka fara kakar wasannin ta na farko a shekarar 2021.
Domin Kari