Wasu daga cikin mutanen da aka kwashe daga yankunansu saboda matsalar ambaliyar ruwa a bara, sun yi barazanar komawa wuraren masu hadari, gabanin kankamar damunar bana.
Dr. Abbas Idriss, Shugaban Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ya yi bayani cewa muddin ba a rika amfani da dokokin tsara birane yadda yakamata ba,to matsalar ambalaiyar ruwa dake cin gidaje ba za ta kau ba.
Masana sun yi gargadin cewa muddin ba a rika amfani da dokokin tsara birane yadda yakamata ba, to matsalar ambalaiyar ruwa dake cin gidaje ba za ta kau ba.
Hukumar Kula Da Yanayi Ta Najeriya Ta Yi Gargadin Cewa Za A Samu Saukar Ruwan Sama Mai Yawa Da Wuri A Bana Tare Da Ambaliya A Wasu Jihohin Kasar. Wasu mutanen miliyan biyu sun rasa muhallansu, yayin da dubban gidaje da gonaki da dukiyoyi na biliyoyin Naira suka lalace.
Dr. Abbas Idriss, Shugaban Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ya yi Karin haske game da matsalar ta ambaliyar ruwa a bana.
Manoma a Najeriya a wurare da dama sun daina zuwa gona saboda fargabar hare-haren ‘yan bindiga.
Hajara Musa Sulaiman a Abuja babban birnin Najeriya, mai kiwon kaji da agwagita ta ce matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a kasar ya tilastawa mata da dama barin sana’ar kiwon dabbobi a gidan gona dake nesa da gari.
A Ghana rashin samun gonaki na daya daga cikin matsalolin da mata masu sha’awar yin noma ke fuskanta.
Ga yawancin mata a Najeriya masu sha'awar noma, rashin samun filin noma wani babban kalubale ne. Amma wasu daga cikinsu su na gudanar da aikin noma ne a kananan filayen dake kusa da gida domin kula da bukatun iyalinsu.
Ummukulthum Kabir Mato, wata kwararriya a fannin aikin gona daga Kaduna a Najeriya ta mana karin haske kan hanyoyin da za a magance wasu daga cikin kalubalen da mata ke fuskanta a fannin aikin gona.
Ummukulthum Kabir Mato, wata kwararriya a fannin aikin gona daga Kaduna a Najeriya ta yi mana karin haske akan wasu kalubale da mata ke fuskanta a wannan fannin a kasar.
Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da kashi daya bisa uku na mata masu aiki a duniya suna aiki ne a bangaren aikin gona.
Domin Kari